Mai Hadishi 9:13-15
13
Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai.
14
An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani.
15
A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan.
Settings