Mai Hadishi 8:14
Ana nuna aya 14 tare da mahallin da ke kewaye.
11
In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba.
12
Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah.
13
Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.
14
Akwai kuma wani abu marar amfani da yake faruwa a duniya, masu adalci sukan sha hukuncin da ya dace da masu mugunta, masu mugunta kuma sukan karɓi sakayyar da ya cancanci masu adalci su samu. Na ce, wannan ma, ba shi da amfani.
15
Saboda haka abin da na ce, shi ne mutum yă ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne yă ci, yă sha, yă ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakin da Allah ya ba shi a wannan duniya.
16
Da na mai da hankalina don in sami hikima in kuma lura da wahalar mutum a duniya, ko da a ce idanunsa ba sa barci dare da rana,
17
sam, ba zai taɓa fahimci abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.
Settings