Daniyel 7:7-14
7
“Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma.
8
“Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya.
9
“Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.
10
Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.
11
“Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta.
12
(An tuɓe sauran dabbobin daga mulkinsu, amma aka bar su su rayu na wani lokaci.)
13
“A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa.
14
Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.
Settings