Skip to content
Daniyel 5:17-24

Daniyel 5:17-24

17
Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.
18
“Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba.
19
Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.
20
Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.
21
Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
22
“Amma kai ɗansa, Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka.
23
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
24
Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options