Daniyel 4:24-27
24
“Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina.
25
Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
26
Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki.
27
Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”
Settings