Daniyel 2:46-49
46
Sai sarki Nebukadnezzar ya fāɗi da fuskarsa har ƙasa a gaban Daniyel domin ya girmama shi ya kuma umarta a miƙa hadaya da kuma hadayar ƙonawa ta turare ga Daniyel.
47
Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”
48
Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima.
49
Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.
Settings