Skip to content
Daniyel 3:1-7

Daniyel 3:1-7

1
Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon.
2
Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa.
3
Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa.
4
Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.
5
Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
6
Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”
7
Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options