Daniyel 11:31-35
31
“Mayaƙansa za su taso su ƙazantar da kagarar haikali za su kuma kawar da hadaya ta kullum. Sa’an nan za su kafa abin banƙyama da yake lalatarwa.
32
Ta wurin daɗin baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi.
33
“Waɗanda suke da hikima za su wayar da kan mutane da yawa, duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.
34
Sa’ad da suka fāɗi, za su sami ɗan taimako, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.
35
Waɗansu masu hikima za su yi tuntuɓe, don a tsabtacce su, a tsarkake su, su yi tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.
Settings