Skip to content
Daniyel 11:21-30

Daniyel 11:21-30

21
“Magājin wannan sarki zai zama wani mutumin banza wanda ma bai fito daga gidan sarauta ba. Zai taso ba zato ba tsammani, yă ƙwace sarautar ta hanyar zamba.
22
Sa’an nan zai shafe mayaƙa masu yawa a gabansa; zai hallaka har da waɗanda suke mulki na alkawari.
23
Bayan ƙulla yarjejjeniya da shi, zai yi zamba cikin aminci, kuma zai sami damar hawan mulki da goyon baya mutane kaɗan.
24
Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai.
25
“Tare da babbar rundunar mayaƙa zai yi ƙarfin hali yă far wa sarkin Kudu da yaƙi. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya.
26
Waɗanda suke ci daga tanadin sarki za su yi ƙoƙari su hallaka shi; za a share mayaƙansa, kuma za a kashe mutane masu yawa a yaƙin.
27
Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.
28
“Sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai girma, amma zuciyarsa za tă yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai ɗauki mataki a kan wannan abu sa’an nan yă koma ƙasarsa.
29
“A ƙayyadadden lokaci zai sāke kai wa Kudu hari, amma a wannan karo abin da zai faru zai sha bamban daga abin da ya faru can baya.
30
Jiragen ruwa yammancin bakin teku za su yi gāba da shi, zuciyarsa kuwa za tă yi sanyi. Sa’an nan zai juya ya huce haushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai komo yă nuna jinƙai ga waɗanda suka juya wa tsattsarkan alkawari baya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options