Skip to content
Daniyel 1:1-6

Daniyel 1:1-6

1
A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya.
2
Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa.
3
Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane.
4
Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.
5
Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima.
6
Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options