Kolossiyawa 2:1-11
1
Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba.
2
Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa,
3
a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.
4
Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki.
5
Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.
6
To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,
7
ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
8
Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
9
Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata,
10
an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.
11
A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.
Settings