Amos 3:10-15
10
“Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”
11
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”
12
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”
13
“Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.
14
“A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa
15
Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji.
Settings