Ayyukan Manzanni 8:39
Ana nuna aya 39 tare da mahallin da ke kewaye.
36
Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?”
38
Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.
39
Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.
40
Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.