Ayyukan Manzanni 28:30
Ana nuna aya 30 tare da mahallin da ke kewaye.
27
Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’
28
“Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!”
30
Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa.
31
Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.
Settings