Skip to content
Ayyukan Manzanni 28:17-29

Ayyukan Manzanni 28:17-29

17
Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa.
18
Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba.
19
Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba.
20
Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.”
21
Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai.
22
Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.”
23
Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa.
24
Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba.
25
Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa,
26
“ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”
27
Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’
28
“Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options