Skip to content
Ayyukan Manzanni 23:6-10

Ayyukan Manzanni 23:6-10

6
Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.”
7
Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu.
8
(Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.)
9
Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?”
10
Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options