Skip to content
Ayyukan Manzanni 23:23-35

Ayyukan Manzanni 23:23-35

23
Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai saba’in da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.
24
Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.”
25
Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka,
26
Kalaudiyus Lisiyas. Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis. Gaisuwa.
27
Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne.
28
Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu.
29
Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a daure shi.
30
Sa’ad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka.
31
Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris.
32
Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja.
33
Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus.
34
Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne,
35
sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Sa’an nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options