Ayyukan Manzanni 23:12-22
12
Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus.
13
Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci.
14
Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus.
15
Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.”
16
Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus.
17
Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.”
18
Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan. Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.”
19
Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?”
20
Saurayin ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus.
21
Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.”
22
Sai shugaban ƙungiyar sojan ya sallami saurayin ya kwaɓe shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka faɗa mini wannan.”
Settings