Ayyukan Manzanni 23:31-35
31
Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris.
32
Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja.
33
Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus.
34
Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne,
35
sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Sa’an nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus.
Settings