Ayyukan Manzanni 21:31-40
31
Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.
32
Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
33
Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a daure shi da sarƙoƙi biyu. Sa’an nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.
34
Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja.
35
Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.
36
Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”
37
Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai ya amsa ya ce, “Ka iya Girik ne?
38
Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ’yan ta’ada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”
39
Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”
40
Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Arameyanci,
Settings