Ayyukan Manzanni 10:9-16
9
Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a.
10
Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa.
11
Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu.
12
Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama.
13
Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”
14
Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”
15
Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”
16
Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama.
Settings