2 Sama’ila 3:1-16
1
Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi.
2
An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;
3
na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;
4
na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;
5
na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.
6
Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu.
7
To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”
8
Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?
9
Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.
10
Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.”
11
Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.
12
Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”
13
Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”
14
Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”
15
Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.
16
Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.
Settings