Skip to content
2 Sama’ila 21:1-14

2 Sama’ila 21:1-14

1
Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.”
2
Sai sarki ya tattara Gibeyonawa ya yi musu magana. (To, Gibeyonawa ba sashen Isra’ilawa ba ne, amma mutanen Amoriyawa ne da suka ragu, waɗanda Isra’ila ta rantse za tă bari da rai, amma Shawulu cikin kishinsa don Isra’ila da Yahuda ya yi ƙoƙari yă hallaka su duka.)
3
Dawuda ya ce wa Gibeyonawa, “Me zan yi muku? Yaya zan yi kafara domin ku sa wa masu gādon Ubangiji albarka?”
4
Gibeyonawa suka ce, “Ba mu da ’yanci mu nemi zinariya ko azurfa daga wurin Shawulu ko gidansa, ba mu kuwa da wani ’yanci mu sa a kashe wani a Isra’ila.” Dawuda ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”
5
Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya hallaka mu ya kuma yi mana makirci don kada mu kasance tare da Isra’ilawa ko’ina a cikin ƙauyukansu,
6
a ba mu zuriyarsa maza bakwai, mu kashe su, mu kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji a Gibeya na Shawulu wannan zaɓaɓɓen Ubangiji.” Sai sarki ya ce, “Zan ba ku su.”
7
Sarki ya ware Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu, saboda rantsuwar da take tsakanin Dawuda da Yonatan, ɗan Shawulu a gaban Ubangiji.
8
Amma sarki ya ɗauki Armoni da Mefiboshet, ’ya’ya biyu maza waɗanda Rizfa ’yar Aiya ta haifa wa Shawulu, tare da ’ya’ya maza biyar na Merab ’yar Shawulu, waɗanda ta haifa wa Adriyel ɗan Barzillai, mutumin Mehola.
9
Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir.
10
Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba.
11
Da aka gaya wa Dawuda abin da Rizfa ’yar Aiya ƙwarƙwaran Shawulu ta yi,
12
sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.)
13
Dawuda ya kawo ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga can, a kuma aka tattara dukan ƙasusuwan waɗanda Gibeyonawan suka kashe, suka kuma rataye.
14
Suka binne ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan a kabarin Kish, mahaifin Shawulu, a Zela a Benyamin. Suka kuma yi kome da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya ji addu’arsu a madadin ƙasar.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options