2 Sama’ila 10:1-7
1
Ana nan sai sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa Hanun kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
2
Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan yi wa Hanun ɗan Nahash alheri kamar yadda mahaifinsa ya yi mini.” Saboda haka sai Dawuda ya aiki jakadu su yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa,
3
sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.”
4
Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su.
5
Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.”
6
Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob.
7
Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings