2 Sama’ila 10:15-19
15
Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu.
16
Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer.
17
Da aka gaya wa Dawuda wannan, sai ya tattara dukan Isra’ila, ya ƙetare Urdun, ya je Helam. Arameyawa suka ja dāgār yaƙinsu, suka kara da Dawuda.
18
Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can.
19
Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu. Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa.
Settings