Skip to content
2 Sarakuna 23:19-25

2 Sarakuna 23:19-25

19
Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji.
20
Yosiya ya yayyanka dukan firistoci na waɗannan masujadan kan tuddai, ya kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kansu. Sa’an nan ya koma Urushalima.
21
Sarkin ya ba da umarnin nan ga dukan mutane, cewa, “Ku yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, yadda aka rubuta a Littafin Alkawari.”
22
Ba a taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa haka ba, tun zamanin da masu shari’a suke aiki a matsayin sarakuna, ko a kwanakin sarakunan Isra’ila, ko na Yahuda.
23
Amma a shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yosiya, aka yi Bikin Ƙetarewan nan ga Ubangiji a Urushalima.
24
Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.
25
Babu wani sarki kafin Yosiya, ko kuma a bayansa, wanda ya juya ga Ubangiji da dukan zuciyarsa, da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa bisa ga shari’ar Musa, kamar yadda ya yi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options