2 Sarakuna 23:15-20
15
Har ma da bagaden Betel, masujadan kan tudun da Yerobowam ɗan Nebat ya yi, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Wannan bagade da masujadan kan tudun ma ya kawar, ya ƙone masujadan kan tudun, ya niƙa su, ya kuma ƙone ginshiƙin Ashera.
16
Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa.
17
Sarkin ya yi tambaya, ya ce, “Wane kabari ke nan nake gani?” Mutanen birnin suka ce, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuda, shi ne ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”
18
Sai ya ce, “Ku rabu da shi, kada wani yă dami ƙasusuwansa.” Saboda haka suka bar kasusuwansa, da na annabin da ya fito Samariya.
19
Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji.
20
Yosiya ya yayyanka dukan firistoci na waɗannan masujadan kan tuddai, ya kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kansu. Sa’an nan ya koma Urushalima.
Settings