2 Sarakuna 23:4-14
4
Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.
5
Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari.
6
Ya ɗauke ginshiƙin Ashera daga haikalin Ubangiji zuwa Kwarin Kidron can bayan Urushalima, ya ƙone shi a can. Ya niƙa shi sai da ya zama toka, sai ya watsar da ƙurar a filin kabarin talakawa.
7
Ya kuma rurrushe mazaunan karuwai mazan haikali waɗanda suke a haikalin Ubangiji, da kuma inda mata suke yi wa Ashera saƙa.
8
Yosiya ya kawo dukan firistoci daga garuruwan Yahuda, ya kuma lalatar da masujadan kan tuddai daga Geba har zuwa Beyersheba, inda firistoci suke ƙona turare. Ya rurrushe matsafai a ƙofofi shigan gari na mashigi zuwa Ƙofar Yoshuwa, gwamnan birnin, wanda yake a hagu da ƙofar birnin.
9
Ko da yake firistocin masujadan kan tuddai ba su yi hidima a bagaden Ubangiji a Urushalima ba, sun ci burodi marar yisti tare da sauran firistoci.
10
Ya lalatar da Tofet, wanda yake a Kwarin Ben Hinnom, don kada kowa yă iya yin amfani da wurin don yă miƙa hadayar ɗansa, ko ’yarsa a wuta ga Molek.
11
Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.
12
Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.
13
Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon.
14
Yosiya ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya rurrushe ginshiƙan Asheransu, ya baza ƙasusuwan mutane a can.
Settings