2 Sarakuna 16:17-20
17
Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse.
18
Ya kawar da rumfa Asabbacin da aka gina a haikalin, ya kuma kawar da mashigin sarki na waje da haikalin Ubangiji, duk dai don yă gamshi sarkin Assuriya.
19
Game da sauran ayyukan mulkin Ahaz, abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
20
Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Settings