2 Sarakuna 15:1-4
1
A shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Yerobowam sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya, sarkin Yahuda ya fara mulki.
2
Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya daga Urushalima.
3
Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yadda mahaifinsa Amaziya ya yi.
4
Amma bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane kuwa suka yi ta yin hadaya da ƙona turare a can.
Settings