2 Sarakuna 15:8-12
8
A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Zakariya ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki wata shida.
9
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba.
10
Sai Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zakariya maƙarƙashiya. Ya tasam masa a gaban jama’a, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.
11
Game da sauran ayyukan mulkin Zakariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
12
Ta haka maganar Ubangiji da ya yi wa Yehu ta cika, wadda ya ce, “Zuriyarka za tă zauna a kursiyin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
Settings