2 Sarakuna 11:10-16
10
Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.
11
Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.
12
Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”
13
Sa’ad da Ataliya ta ji surutun matsara da na mutane, sai ta tafi wurin mutanen a haikalin Ubangiji.
14
Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”
15
Yehohiyada ya umarci komandodin sojoji waɗanda suke lura da mayaƙa, ya ce, “Ku fitar da ita daga cikinku, ku kuma kashe duk wanda ya bi ta.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada a kashe ta a cikin haikalin Ubangiji.”
16
Saboda haka suka kama ta yayinda ta kai inda dawakai sukan shiga filin fada, a can kuwa aka kashe ta.
Settings