2 Korintiyawa 5:11-15
11
To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.
12
Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya.
13
In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne.
14
Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.
15
Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
Settings