2 Korintiyawa 2:1-4
1
Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba.
2
Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba?
3
Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.
4
Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.
Settings