Skip to content
2 Korintiyawa 10:7-11

2 Korintiyawa 10:7-11

7
Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke.
8
Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki.
9
Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna.
10
Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.”
11
Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options