Skip to content
2 Tarihi 30:6-12

2 Tarihi 30:6-12

6
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.
7
Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani.
8
Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku.
9
In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.”
10
’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a.
11
Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima.
12
Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options