Skip to content
2 Tarihi 25:11-16

2 Tarihi 25:11-16

11
Sa’an nan Amaziya ya yi ƙarfin hali ya jagoranci mayaƙansa zuwa Kwarin Gishiri, inda ya kashe mutanen Seyir dubu goma.
12
Mayaƙan Yahuda suka kuma kama mutane dubu goma da rai, suka ɗauke su zuwa ƙwanƙolin dutsen, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa suka yi kaca-kaca.
13
Ana cikin haka, sai rundunar da Amaziya ya mai da su gida, waɗanda ba a bari suka tafi yaƙin ba, suka kai wa garuruwan Yahuda daga Samariya zuwa Bet-Horon hari. Suka kashe mutane dubu uku suka kwashe ganima mai yawan gaske.
14
Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa.
15
Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?”
16
Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options