2 Tarihi 2:4-6
4
Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila.
5
“Haikalin da zan gina zai zama mai girma, domin Allahnmu ya fi dukan sauran alloli girma.
6
Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba?
Settings