1 Sama’ila 6:17-20
17
Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.
18
Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh.
19
Amma Allah ya kashe waɗansu mutum saba’in na mutanen Bet-Shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawarin Ubangiji. Mutane kuwa suka yi makoki domin Ubangiji ya hallaka mutane da yawa.
20
Mutanen Bet-Shemesh suka yi tambaya suka ce, wa zai iya tsaya a gaban Ubangiji Allah Mai Tsarki? Wurin wa akwatin alkawari zai je daga nan?
Settings