Skip to content
1 Sama’ila 31:6-10

1 Sama’ila 31:6-10

6
Shawulu da yaransa uku da mai ɗaukar makamansa da dukan mutanensa suka mutu a rana ɗaya.
7
Sa’ad da Isra’ilawa na bakin kwari da waɗanda suke hayin Urdun suka ga sojojin Isra’ila suna gudu, Shawulu da yaransa uku kuma duk sun mutu, sai suka bar mallakansu suka sheƙa da gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka mamaye wuraren.
8
Kashegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka tarar Shawulu da ’ya’yansa uku duk sun mutu, a dutsen Gilbowa.
9
Suka sare kansa suka tuɓe makamansa, suka aika manzanni a dukan ƙasar Filistiyawa, su ba da labarin a haikalin allolinsu da cikin mutanensu.
10
Suka ajiye makaman Shawulu a cikin haikalin gumakan Ashtarot. Suka kafa gawarsa a kan katanga Bet-Shan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options