1 Sama’ila 30:20-31
20
Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.”
21
Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bari a bakin Kwarin Besor, sai suka taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su, sai ya gaishe su.
22
Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum yă ɗauki matarsa da ’ya’yansa yă tafi.”
23
Dawuda ya ce, “A’a, ’yan’uwana ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ya tsare mu, ya kuma bashe sojojin da suka yi gāba da mu a hannuwanmu.
24
Wa zai goyi bayanku a kan wannan al’amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya, rabonsu zai zama daidai.”
25
Dawuda ya sa wannan tă zama dawwammamiyar farilla ga Isra’ila tun daga wannan rana har yă zuwa yau.
26
Da Dawuda ya iso Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuda da rabo daga cikin ganimar ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”
27
Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir,
28
da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa,
29
da Rakal, da garuruwan Yerameyelawa, da garuruwan Keniyawa,
30
da Horma, da Bor-Ashan, da Atak,
31
da Hebron, da dukan wuraren da Dawuda da mutanensa suka taɓa zagawa.
Settings