1 Sama’ila 29:1-4
1
Filistiyawa suka tattara dukan rundunoninsu a Afek. Isra’ila kuwa suka yi sansani kusa da maɓulɓular da take Yezireyel.
2
Sa’ad da sarakuna Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari-ɗari da na dubu-dubu. Dawuda da mutanensa suna biye a baya tare da Akish.
3
Komandodin Filistiyawa suka ce, “Waɗannan Ibraniyawa kuma fa?” Akish ya ce, “Wannan shi ne Dawuda hafsan Shawulu, sarkin Isra’ila. Yana nan tare da ni shekara guda ke nan. Ban kuwa taɓa samunsa da wani lahani ba tun daga ranar da ya bar Shawulu.”
4
Amma komandodin Filistiyawa suka yi fushi, suka ce, “Ka sa mutumin nan yă koma zuwa wurin da ka ba shi yă zauna. Ba zai bi mu zuwa wurin yaƙi ba. Yana iya juya a kanmu lokacin yaƙin. Zai iya yin amfani da wannan zarafi yă ciccire kawunanmu don yă faranta wa maigidansa rai?
Settings