1 Sama’ila 25:2-11
2
A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.
3
Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne.
4
Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.
5
Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,
6
su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi!
7
“Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata.
8
Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”
9
Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.
10
Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.
11
Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”
Settings