Skip to content
1 Sama’ila 22:9-19

1 Sama’ila 22:9-19

9
Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob.
10
Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”
11
Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki.
12
Shawulu ya ce, “Ka saurara yanzu, ɗan Ahitub.” Ya amsa ya ce, “Ina saurara, ranka yă daɗe.”
13
Shawulu ya ce masa, “Don me ka gama baki da ɗan Yesse a kaina har ka ba shi burodi da takobin (Goliyat), ka kuma roƙi Allah don yă tayar mini, yă kuma yi fakona kamar yadda yake yi yau?”
14
Ahimelek ya ce wa sarki, “A cikin bayinka duka, wa ke da aminci iri na Dawuda, surukin sarki, shugaban jarumanka wanda ake girmamawa da gaske a gidanka?
15
A wannan rana ce da na fara roƙon Allah saboda shi? Kada sarki yă zargi bawansa ko wani daga iyalin mahaifinsa, gama bawanka bai san kome a kan dukan waɗannan al’amura ba.”
16
Amma sarki ya ce, “Lalle Ahimelek za ka mutu, da kai da dukan iyalin mahaifinka.”
17
Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.” Amma ma’aikatan sarki ba su yarda su sa hannu su kashe firistocin Ubangiji ba.
18
Sai sarki ya umarce Doyeg ya ce, “Ka juya ka kakkashe firistocin.” Doyeg mutumin Edom ya juya ya kakkashe firistocin. A ranar kuwa ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke sanye da efod na lilin.
19
Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakuna, da kuma tumaki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options