Skip to content
1 Sama’ila 18:3-12

1 Sama’ila 18:3-12

3
Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa.
4
Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa.
5
Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.
6
Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.
7
Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”
8
Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?”
9
Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.
10
Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.
11
Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.
12
Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options