1 Sama’ila 10:10-13
10
Da suka iso Gibeya, jerin gwanon annabawa suka sadu da shi Ruhun Allah kuma ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga yin annabci tare da su.
11
Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi a dā suka gan shi yana annabci tare da annabawa, sai suka tambayi juna, suka ce, “Me ya faru da ɗan Kish? Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”
12
Wani mutumin da yake zama a can ya ce, “Wane ne kuma mahaifinsu?” Ta haka sai wannan ya zama karin magana cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa?”
13
Bayan da Shawulu ya gama annabci sai ya haura ya tafi tudu.
Settings