1 Bitrus 5:1-9
1
Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana.
2
Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima;
3
ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken.
4
Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.
5
Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”
6
Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.
7
Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
8
Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.
9
Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.
Settings