1 Sarakuna 6:29-35
29
A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu.
30
Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya.
31
Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar.
32
A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya.
33
Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure.
34
Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai.
35
Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa.
Settings