1 Sarakuna 6:16-22
16
Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama.
17
Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne.
18
An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
19
Ya shirya wuri mai tsarki na ciki can cikin haikali don yă sa akwatin alkawarin Ubangiji a can.
20
Tsawon wuri mai tsarki na ciki kamu ashirin, fāɗin kamu ashirin, tsayin kuma kamu ashirin. Ya dalaye cikin da zinariya zalla, ya kuma dalaye bagade al’ul ɗin.
21
Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya.
22
Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya.
Settings