1 Sarakuna 5:9-11
9
Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”
10
A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata.
11
Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.
Settings